Bookmark and Share

Matsalar kasar pakistan

 

Al Gaddafi na hira Hausa

Image description

Muammar Al Gaddafi na hira Hausa

Muammar Al Gaddafi speaks Hausa 

Audio |  |

Video |  | 

Image description


Matsalar kasar pakistan


 

18.12.2008

Yahudawa da amurukawa basu so ba kasar Pakistan ta kera bomb din nuklea . Amma a cikin basu sani ba sai ga Pakistan ta kera  makaman nuklea. In da sonsu ne da haka bay faru ba.  Amma dai da ya faru sai suka ga layhin kanunsu da  kungiyoyin asirinsu . Sai suka fara aza ma juna layhi. Suka sanya ma bomb din suna “bomb din islama”.

  Sun yi komi domin hana Pakistan ta kera wannan bomb har ma sofon ministan kasar amuruka mai kula da harakokin waje kesinger yace ma praministan kasar Pakistan thoul farouk  ali buto “ idan ka kera bomb din nuklea zani yi dakai misali ga sarwa”.


  Sai aka rataye buto domin kowa ya ji soron kera bomb. Bayan haka sai aka kashe Diyaou Al-hak da Bonazir diyar Buto.Har yanzu kuma ba akawo karshen kashe-kashen ba.

    Amma dan sabodami Amuruka da israilawa basu son kasar Pakistan ta mallaki bomb din nuklea?

   Kasar Pakistan kasar musulumci ce ; tushenta ma addinin islamane .Ba abinda ke iya hada kan kasar Pakistan kawar muslumci. Dan hakane suke da tsanani kan addini. Inda ba dan addinin islama ba da ba al-ummar Pakistan. Kawar yadda addinin yahudawa yake ga israilawa haka addinin islama yake ga yan Pakistan shine tushen  zamansu. Kasar chana , alal misali, kasace da addini ko da rishin shi. Haka kasar Iran da ta Turki. Amma ita Pakistan daban take.


 In bada iddinin muslumci ba kasar Pakistan saboda addini shine dalilin rabuwar Pakistan da kasar India. Gaskiyace bomb in kasar Pakistan bomb ce ta islama. Musulumci ga yan Pakistan ba wai addini ne ba kawai yariga ya zama komai nasu.


    Al’ummar kasar Pakistan gami ne na Sandinawa da Banjabyawa da Botharyawa Sra’ikyawa da Blushinyawa da Hazrayawa da Makranyawa da Kashmiryawa da  Pashtunyawa da Handukyawa da Afganawa da wasu kabiloli na yankuna dake kusan Afganistan wa-anda yazamanto su ba na Pakistan bane kuma ba na Afganistan ba. Wa’annan kabilolin ko wace tana da yarinta; al-amarinda ke haddasa rishin gane ma juna.


   Kasar Pakistan na fuskantar masaloli a yankin da take : daga kasar Iran mai addinin muslumci na shi’a da ga kuma kasar India dake da addinin Hindu da na buda. Inda addinin islama yake a kasar Pakistan ba a yanki bane mai kunciyar hankali. Addinin yana a yanki da ake tsokana. Wannan yankin na fuskantar babar masala da ta shafi  addinin islama dake shine tushen zaman al-ummar kasar Pakistan musaman ga fuskantar addinin hindu da na buda da kuma fuskantar tsautsawan ra’ayi. Daga nan ne aka kafa kungiyoyin islama masu tsautsawan ra’ayi. Wa’annan kungiyoyin suka cudu da kabilolin Afganistan da kungiyar alka’ida da Ben Laden sai suka kare shi. Wa’annan kungiyoyin  kawar “ jama-ar musulmi” da kungiyar” masanan  islama” na nuna tsautsawan ra’ayoyinsu. Israilawa da Amurukawa na ganin cewa wa’annan kungiyoyin na iya sabbaba musu masaloli in suka haw iko. In wa’annan kungiyoyin suka haw iko, al’amarinda ke iya wakana, zasu iya sabbabama isra’ilawa da amurukawa matsala ba kawar sauran kungiyoyin siyasaba. Dan saboda a ganin israilawa da amurukawa kungiyoyin siyasa sun san abinda suke yi. Amma sai yazamanto ba tabbas bane su tsaya a  iko har kulun.


   In dai wa’annan kungiyoyi masu tsausawan ra’ayi suka haw iko ,bomb din nuklea zata shiga hanunsu. To wannan shine fa  matsalar Pakistan  .Isra’ilawa da amurukawa sai dai su fuskanci wannan masalar domin warwareta. Dan haka ne suke dasa adawa tsakanin Pakistan da India. Sai su tabbatarma Pakistan cewa makiyanta hindu ne ba yahudawa ba da almasihu.kenan  ga sune ya kamata a tinkarasda  bomb din nuklea. Haka kuma sai suce ma hindu ga kune kasar Pakistan ke son anfani da bomb in nuklea ba ga yahudawa ba ko ga amurukawa ba.


   Siyasar israilawa na neman ta sa kasar Pakistan ta damu da ta India, haka India ta damu da Pakistan. Sai su kafa abutta da yan pakistan . su kotomta musu cewa zasu temaka musu domin fuskantar  makiyinsu hindu na india. Haka zalika sai su je ga hindus su dasa abutta da hulda dasu domin fuskantar musulmin pakistan. Gurin wannan siyasar shine dasa rikici da zai sa kasashen biyu su damu da juna har kullum . har ma sukai ma juna hari yadda ko wace zata kare makammanta na nuklea ga ta biyun. Ina tammahar cewa amuruka ba zata bada gudunmuwarta ga warware rikicin kashmir ba , kuma bata hatan ya warware. Su ko israilawa har abada zasu tsaya bayan  wannan rikicin suna kara mishi huta.


   A cikin ko wane hali dai matsalar bomb in kasar Pakistan zata ci gaba. Amurukawa da israilawa zasu ci gaba da neman warware  wannan matsalar ta ko wace hanya har tashin kiyama

 

 

Bookmark and Share