HUDUBAR MADUGUN CANJI GA DALIBAN JAMI'AR OXFORD DAKE KASAR BIRTANIA KAN MATSAYIN NAHIYAR AFIRKA A KARNI NA ASHIRIN DA DAYA A RANAR
Muammar Al Gaddafi na hira Hausa
Muammar Al Gaddafi speaks Hausa
HUDUBAR MADUGUN CANJI GA DALIBAN JAMI'AR OXFORD DAKE KASAR BIRTANIA KAN MATSAYIN NAHIYAR AFIRKA A KARNI NA ASHIRIN DA DAYA A RANAR
16.05..2007
Jama'a barkammu da yamma … Da farko godiya ga wadanda suka shirya wannan taro da dalibai da kuma malaman jami'ar Oxford, Ina fatan zamu cigaba da ganawa lokaci-lokaci domin mu taimakawa duniya wajan fuskantar kalu bale da kuma matsaloli daban-daban a bangarorin siyasa da tattalin arziki da kuma zamntakewar dan adam.
Kunnemi da nayi huduba game da nahiyar Afirka a karni na ashirin da daya .. Ina fatan wannan huduba tawa zata amfani duniya baki daya ba wai ku daliban jami'arOxfordko kuma jama'ar Afirka kawaiba.
Adalokacin yakin cacar baka, manyan kasashan duniya masu karfi, suna fada da juna wajan zawarcin nahiyar Afirka, ina nufin kudancin turai da gabashinta Rasha da Amurka ko kuma kungiyar tsaron Nata da kuma ta worso.
Wannan al'amari ya kawo babbar matsala a nahiyar Afirka da kuma duniya baki daya.
Nahiyar Afirka ta cutu kwarai da gaske a wancan taho mugama, tsakanin kasar Amurka da kuma kishitarta tarayyar Soviet, wadannan man kasashe suna zawarcin nahiyar Afirkane domin kwasar dunbin arzikin karkashin kasa da Allah ya hore mata, da kuma ganin nahiyar tazama yan amshin shatan su.
Wannan taho mugama ya cutar da mu baki daya, bai kuma amfanawa duni komaiba, a tun karon farko taho mugaman ya samo asaline a tsakaninsu can wato kasashan yammacin turai da kuma gabashinta, daga bisanine al'amarin ya kawo garemu, inda wasu kasashan Afirka ke bin tsarin siyasar gabashin turai yayinda sauran kasashan ke bin siyasar kudancin turai.
Hakan ya yi sanadiyar haihuwar guzuma tsakanin nahiyar Afirka da kuma manyan kasashan na duniya.
Tarayyar Soviet da kuma amurka sunyi asarar dunbin dukiya wajan ganin kowace daya daga cikinsu ta mamaye Afirka, wannan shine ummul haba'isi na rashin zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya baki daya, idan ka cire nahiyar turai sauran kasashan duniya sun fuskanci yake-yake da fadace-fadace da kuma juyin mulki.
Wannan yafaru a nahiyar turai da nahiyar Afirka musamman arewacin nahiyar kai harma da nan wajan da muke tsaye a ayu.
Nufina shine idan aka sami taho mugama da kuma fadace-fadace a wasu yankuna na duniya kamar yadda ya faru a Afirka da kuma turai ta masifar takan shafi dunita baki daya.
Anan ina fatan duniya zata fahimta, za kuma ta koyi darasi gameda matsalolin da suka faru a baya, ta kuma canza salon tafiya.
Adakasashan nahiyar turai sun fuskanci rarrabuwar kai da kuma yake-yake a tsakaninsu, sakamakon hadinkan kasashan a yanzu ya kawo masu cigaban tattalin arziki da kuma na siyasa.
Nahiyar turai tana a tsakanin tarayyar Rasha da kuma kasar Amurka, duk da haka kuwa an sami zaman lafiya a nahiyar.
Ita kuwa nahiyar Afirka duk da kokarinta na ganin ta kubuta daga taho mugama a tsakanin manyan kasashe a lokacin yakin cacar baka.
Saidai kash bisa dukkannin alama ja-na-ja a tsakanin manyan kasashan duniya yana so ya mayar da nahiyar ruwa.
Al'amarin ya canza sabon salo a wannan karon kasar china da kuma Amurka suke so suyi taho mugama a nahiyar.
Saboda haka naga ya zamo wajibi na zamo farkon wanda zai fara fadakarwa game da wannan … wasu suna jin kunya ko kuma tsoron futowa fili suyi magana game da wannan batu.
Tamkar mutumin dake da ciwone yake boyewa da nufin bayyanashi a wani lokaci nan gaba.
Ni bana wata-wata wajan fadar gaskiya ga Afirka ko kuma duniya baki daya.
A yau Afirka ta wayi gari ta tsinci kanta a matsayin dandalin fito-na-fito a tsakanin wasu manyan kasashan daban.
Wannan fito-na-fito zai wahalar da kasashan biyu wato Amurka da kuma china.
Kowace daya daga cikin kasashan biyu ta shiga nahiyar Afirka ta hanya daban-daban itadai Amurka tayi amfani da karfin soji wajan shiga wannan nahiya, inda taketa fafutukar neman wajan da zata kafa sansanonin sojinta, da nufin yin shishshigi a al'amuran kasashe, da hujjar kare hakkin dan adam, maimakon hakan kamata yayi ta fara kare hakkin dan adam a can kasarta kafin wasu kasashan.
Tana nanata kare hakkin dan adam da kuma demokuradiyya alhali babu demokuradyya a Amerika.
Idan akakamadaya daga cikin yan amshin shatanta da lefin leken asirin wata kasa, sai kaji Amurka na hayaniya, saboda menene kuka kamashi? Mai yayi maku? Kuma a'inane kuka daure shi?
Shin akwai wata kasa da zata iya tuhumar Amurka da lefinkamawani mutum tare da kuma kulle shi? Idan babu to wa yabawa ita Amurka ikon yiwa sauran kasashe katsa landan.
Wannan itace hanyar da Amurkakanyi amfani da ita wajan shiga nahiyar Afirka, wata ta hanyar amfani da karfin hatsi.
Yayinda ita kuwa chinakanshiga Afirka ta hanyar lumana … ko da yake dukkanninsu biyun sababbin yan mulkin mallakane, wadanda ke fafutukar yin wawaso ga dunbin arzikin da Allah ya huwacewa wannan nahiya.
Ita china baruwanta da batun hakkin dan adam, ko hakkin fadar albarkacin baka, ko kuma mulkin demokuradiyya.
Haka kuma china bata amfani da karfin soji wajan shiga wata kasa, ba kuma ta shishshigi a harkokin cikin gidan kasashe.
Saboda ita ta hanyoyin lumana take bi, ahalin da ake ciki akwai fiye da kamfanonin china600 anahiyar Afirka, a wasu kasashan nahiyar kuwa tuni yan china sun yi kakagida.
Jama'a Afirka sun budewa china kofofinsu saboda bata nuna karfi, a lokaci guda suna dari-dari da kasar Amurka saboda fun karfi da take nunawa.
Wannan ya nuna yadda Amurka ta jahilci harkokin rayuwa aduni baki daya.
Saboda hakane ita Amurkan take kwasar kashinta ahannu a kasashen da take yiwa shigar karfi kamar yadda ya afku a kasarVietnam, da Somalia, da kuma Iraki a yau.
Yayin da ita kuwaChinatake amfani da hikima wajan shiga kasashe kamar yadda al'amarin ke faruwa a kasashan Afurka, inda take kwasar ganima cikin rowan sanyi.
Wasu suna da ra'ayin cewa lokaci yayi da zamu jawo kasar china a jika, mu kuma yi nesa da kasar Amurka, sun manta da cewa mukin mallaka duka gudane, banbancinsu kawai wannan na amfani da lumana yayin da gudar ke amfani da karfin hatsi.
Wasu na lale maraba da kasar china, mu kuwa anamu bangaren muna neman wanda zai nesantar da mu daga jarabar kasar Amurka.
Zamu goyi bayan china akan sharadin bazata maidamu karkashin mulkin mallakartaba, kuma bazata kosher albarkatun kasashanmu ba arha katsal.
Idan muka gudanar da kuri'ar jin ra'ayin jama'a, ba shakka jama'a zasu zabi kasar china, saboda mutane sun gaji da fin karfin da Amurka ke nunawa a kasashan duniya da dama, ta hanyar amfani da karfin soji wajan yin shishshigi ga al'amuran cikin gidan kasashe.
Wannan dayace daga cikin matsalolin da muke fuskanta a yau.
Hadin kai a tsakanin kasashan Afirka shi zai kawo cigaba a wannan nahiya … kamar dai yadda nahiyar turai take a yau, ya kawo cigaba ga kasashan yammacin turai da kuma duniya baki daya, bakajin wasu rigingimu ko fadace-fadace.
Na san da cewa har yau akwai rundunonin sojin Amurka da ke kaka gida a wasu daga cikin kasashan yammacin turai, wannan batune wanda ya shafi turawa kadai, duk da yake al'amarin yana barazana ga zaman lafiya a turai da kuma kasashan da ke iyaka da koginMediterranean.
Daga karshe dai kasashan turai sun hada kansu, suna amfani da kudi guda, tsarin siyasa guda, wannan ya kawo zaman lafiya a duniya baki daya.
Muna bukatar ganin kasashan Afurka sun hada kansu wuri guda, ta yadda zasu sami damar kafa asusu guda, su samarwa kasashansu kudi guda, tasrin tsaron kasashansu guda, tsarin kasuwanci guda, da hakane zasu iya taimakawa tattalin arzikin kasashansu.
A halin da ake ciki dai kimanin kasashan Afirka hamsin na amfani da takardun kudadai hamsin, manyan bankuna hamsin, tsarin kasuwanci hamsin, basu da wani tasiri a duniya.
Idan ka dau tattalin arzikin kasar Malawi da Gambia da kumaGuinea-Bissauka kwatantashi da na daya dagacikin manya-manyan kasashe baka ganin wani tasirinshi.
Tarayyar turai ko Amurka koChinako kuma kasarJapanbazasu tsaya bata lokacinsuba wajan tattaunawa da tawagar kasuwanci ta daya daga cikin kasashan Afirka da muka ambata, kar dai kasaGambia, waceceGambiaa gaban wadannan kasashan?
Idan kuwa akace ga tawagar kasuwancin Afirka ta zo ta sai motoco rabin milyam, to kaga da gudu wadancan manyan kasashe zasu saurareta, domin sunsan akwai amfani mai yawa da zasu samu a karkashinta .. amma idan kuwa kasa dayace, koda kuwaLibyace bazasu damu da itaba, sai dai kawai domin arzikin man petur da Allah ya huwacewaLibya, wannan misali ne zaka iya bugashi akan sauran kasashan Afirka baki daya.
Tarayyar turai ko Amurka koChinako kuma kasarJapanzatafi bawa ministan kasuwancin nahiyar Afirka mahimmanci, ganin cewa babbar kasuwace mai takardar kudi ta baiguda.
Ina fatan ganin manyan kasashan duniya zasu taimaka wajan ganin kasashan Afirka sun hada kansu, sun zamo kasa guda daya tilo, sabo da hakan zai taimaka wajan samar da zaman lafiya tare da kwaciyar hankali a kasashan Afirka da kudancin turai, da kuma duniya baki daya.
Muna maraba da kamfanonin Turai da Amurka daJapanda kumaChinaa nahiyar Afirka, amma bazamu amince da su zo suyi mana kakagida ko milkin mallakaba
A yau Afirka kammu yawaye, munada masana a kowane fanni na rayuwa, ba kaman da ba.
Ina kira ga kasashan da ke kera jiragen yaki da makamai masu lunzami da kuma makaman kare dangi, su bawa Afirka kadan daga cikin kudadan da suke warewa domin kera wadancan miyagun makamai.
Ina kasar Amurka da tarayyar Turai da Japan da kuma kasar Sin ku zo ku mu hada karfi da karfe mu raya kogin Anger na kasar Congo, domin samara da wutar lantarki, ga nahiyar Afirka baki daya, harma mu siyarwa yammacin Turai da kuma kasashan Asiya.
Mai zai hana su kebe mana milyoyin kudi domin samun nasarar wannan gagarumin aiki wanda zai amfani bil adama.
Wannan aikin yafi dacewa ko kere-keren kayan yaki, ko kuma fafutukar neman hakkin fadar albarkacin baka? Gashi kuwa bamu da wani gidan jarida ko radiyo guda mai karfi wanda zai yada ra'ayin mu.
Su zo su taimakamana wajan farfado da kogin Cadi, wannan shine hakkin fadar albarkacin bakin mu.
Na gabatar da bayani a rubuce game da halin da kogin Cadi yake ciki yayin zaman taron duniya kan yanayi da kuma cigaban dan adam, wanda aka gudanar a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta kudu, a halin da ake ciki ruwan wannan kogi ya kafe saura kashi daya cikin dari.
Su zo muhada karfi muyi magudanar ruwa daga kogunan kasashan Kwango da Afirka ta tsakiya da kuma Camaru.
Na yi cikakken bayani da nayi game da kogin na Cadi.
Bayan aikin farfado da kogunan Cadi da na Anger, domin samar da wutar lantarki.
Ina kiran duniya da a ceto kungurmin dajin Kwango daga halaka, wannan dajin da kuma na Amazon dake kudancin Amurka su ke bawa duniya iskar dam u ke shaka ta iskar ( Oxsygen ).
Wadannan sune abubuwan da nake so na ja hankalin duniya gare su a wannan haduwa tamu, na gode game da wannan dama da kuka bani na fadar halin da Afirka ke ciki a yau.
Idan akwai wata magana daban da kuke so mu tattauna to bisimillah, a tare da ni akwai Koran littafi da kuma Farin littafi, idan kuma akwai mai tambaya daga cikin dalibai ko malaman jami'ar Oxford to bisimillah.
- Daya daga cikin mahalarta taro ya mike yace : Madugun canji godiya muke game da wannan cikakken bayani bisa halin da nahiyar Afirka ke ciki, ina so na karanto wata tambaya daga wani dalibi,kanmanyan kasashe masu fada aji .. wai mai yasa bazasuyi amfani da karfiba wajan warware rikice-rikice a Afirka, kamar dai rikicin kasarSomaliako kuma kasarZimbabwe?
- Madugun Canji : madallah .. Dana ina so ka gane cewa kimanin kashi uku cikin hudu na sojojin majalisar dinkin duniya suna aiki ne a nahiyar Afirka saboda rikice-rekice da nahiyar ke fama da shi.
- Agaskiya ummul haba'isin wannan matsala kuwa shine milkin mallaka .. rigingimun da ake fama da su na kabilanci ne, a lokacin dakanAfirka a hade yake, sai gashi yan mulkin mallaka sun zo sun raba mu ya zuwa kashi hamsin, su ka sanya iyakoki a tsakaninmu.
- Misali kasar Abiri-kos (Ivory coast) a da kasar hade take da makociyartaBurkina Faso.. sai gashi yan mulkin mallaka sun raba kasar gida biyu,Upper Volta(Burkina Faso) da kuma Lower Volta (Ivory coast) .. wannan shine ummul haba'isin rikicin kabilanci a tsakanin kasashan biyu.
- Abiri-Kos (Ivory Coast) tana ganin cewa mazauna Arewacin kasarta yan asalin kasarBurkina Fasone, to kaga mulkin mallaka shi ya jawo wannan matsala.
- Haka kuma rikicin dake faruwa a kasashan Rwanda da Burundi da kuma Kwango (Congo) tsakanin kabilun Tutsi da kuma Hutu, milkin mallaka ya kawoshi.
- Bugu da kari kuma milkin mallaka ya kunna wutar rikicin kasar Kwango (Congo) saboda su sami damar kwasar arzikin Daimon ( Diamond ) da kuma yoraniyom (uranium ) da nufin kera makamin kare dangi wanda suka yi amfani da shi akankasarJapan.
- Wannan misali kana iya bugashi akankasarSomalia, turawan mulkin mallaka na kasar Italiya (Italy) da kuma na Birtaniya (Britain) suka raba kasar biyu.
- Italiya (Italy) ta rike Arewacin kasar, yayinda ita kuma Birtaniya (Britain) ta dau kudancin kasar.
- Idan ka dibi Taswirar duniya ( world map ) zaka taras da cewa kasarGambiata samo asalin sunanta ne daga wani kogi dake tsakiyar kasarSenegal.. turawan mulkin mallaka na kasar Biritaniya (Britain) suka yi kaka gida a wajan, suka koyawa yan asalin kasar harshen su na turancin Ingila (England) daga bisani suka yancin kai, su kuma turawan Faranshi ( France ) suka mulki bangaranSenegal.
- Amsar tambayar da ta gabata shine, majalisar dinkin duniya nada isassun dakaru a Afirka da zasu iya kwantar da kowane rikici, mu kasashan mu suna karkashin inuwar kungiyar tarayyar Afirka ne, a shirye muke mu tura sojojin mu ya zuwa kowace kasa idan har kungiyar ( A. U. ) ta bukaci hakan.
- Matsaloli sun wuce yadda muke tunani, a yau Afirka na bukatar hadin kai a tsakanin kasashanta ta yadda zata sami damar maganin matsalolin da milkin mallaka ya jawo mana, kungiyar tarayyar Afirka ta hade ta zamo kasa daya maimakwan kasashe hamsin da muke da su a yau.
- Wannan shine aikin da muka sa a gaba, ba wai aika sojoji zuwa kasashe ba, majalisar dinkin duniya bata daukan nauyin tura dakaru zuwa wata kasa sai har sun amince da yin aiki karkashin inuwarta, wasu kuma basu san ganin sojojin majalisar dinkin duniya a kasashan su, kamar dai kasar Sudan.
- Dalilin su shine dakarun majalisar ta dinkin duniya yan babakere ne, kuma suna aiki ne da umarnin kasar Amurka.
- Daga karshe dai mulkin mallaka ne ya jawo fadace-fadacen kabilanci da muke fuskanta.
- Tambaya ta biyu itace:
- Madugun canji, sunana Tarik ni dan asalin kasar Tunusia ne .. tambayata itace menen alakar da ke tsakanin mulkin demokuradiyya da kuma batun hadin kai a tsakanin kasashe, matsalar yankin sahara da kuma mulkin demokuradiyya .. tayaya ne zamu sami nasarar kafa kasuwa ta bai guda a lokaci guda kuma mu samara da kyakkyawar tsarin demokuradiyya?
- Madugun canji ya amsa da cewa: ina ma dai ace shugabannin kasashe zasu ji wannan tambaya taka kuma suyi aiki da shi.
- Tunanina ya zo daya da tunaninka, saboda haka ne a koda yaushe nake kira ga kasashe da su maida ragamar mulki ga hannun jama'ar kasashen su, ta hakane za'ayi maganin kabilanci a tsakanin al'umma, misali shine tsakanin jama'ar kasar Algeria da kuma yan kasar Moroko ( Morocco ) ba matsala a tsakaninsu, matsala tana tsakanin yan siyasar kasashan biyu.
- Shugabannin kasashe da kuma jami'an tsaronsu sune ummul haba'isin rashin zaman lafiya a duniya.
- Holako da Jankis Khan da Hitler da Napeleon Misolini da kuma Bush .. wadannan sune suka yi amfani da matsayinsu na shugabancin kasa suka kai hari ga wasu al'ummomi daban.
- A yau shiru kake ji a kasar Jamus (Germany) bayan mutuwar Hitler yan kasarshi sun zamo masu san zaman lafiya.
- Haka al'amarin yake a kasar Faranshi ( Farance ) Napeleon ya koya musu akidar mamaye wasu kasashan da nufin mulkin mallaka.
- Saboda haka ni – Madugun canji – ina ganin batunnan da ake na cewa Larabawa da kuma addinin Musulumci sun bude nahiyar Turai a shekarun 300, shima mulkin mallaka ne.
- To mai ya sa daga baya aka kori musulmai daga wadancan garuruwa na turai.
- Wanene ya bada izini? Shugabanni makwadaita masu neman kwasar ganima sune ke bada umarnin yaki da mamaya da kuma mulkin mallaka …
- Tambaya ta gaba : Shin kungiyar tarayyar Afirka zata iya tura dakaru kasarSudanba tare da izinin ilahirin al'ummar kasar ba?
- Madugun canji : Game da yankin Darfur akoda yaushe ni inada ra'ayi daban na fadar gaskiya ta hanyar raha, saboda ni dai bad an siyasa bane, ba kuma jami'in duplomasiyya bane, ni madugune na canji, hakika na yi matukar kokarin ganin na warware rikicin yankin Darfur, sarakunan gargajiya da kuma shugabannin al'umma na wannan yanki sun zo wajena mun tattauna game da hanyar da ta kamata abi domin samun zaman lafiya da kuma kwanciyar hankali a yankin su.
- Matukar kungiyoyin bada agajin gaggawa na kasa da kasa nada sansanoni a yankin Darfur to wutar rikici zata cigaba da ci, kauyawa mazauna yankin naDarfurbazasu so ganin an sasanta wannan rikiciba, matukar ana raba masu abinci kyauta, saboda haka su gaba ta kaisu, rikicin ya cigaba saboda ga abinci ana raba masu kyauta.
- A kasarLibyamun bude tashar jiragen ruwa dake garinBenghazida kuma ta jiragen sama dake garin Kufra domin samun damar isar da taimakon jinkai ya zuwa yankinDarfurta hanyar kasa.
- Yayin da mazauna yankin Darfur suka ji wannan labari sai akace masu maizesa ku dakatar da yaki alhali gag anima zata dinga zuwa maku ta kasarLibya? .. ku cigaba da tada tarzoma da rana kudinga zuwa zangon yan gudun hijra kuna karbar taimako, idan kuma rana ta fadi kukoma kauyukanku kuyi barci.
- Wannan shine abinda yake faruwa aDarfur, matukar za'a dinga turo abinci ana rabawa ga jama'a bazasu so karewar yakinba.
- Bugu da kari kuma kasashen duniya dakan ruwa da tsaki a rigingimun cikin gida na wasu kasashe, kuma kafofin watsa labaru dakanbawa shugabannin yantawaye damar fadar abinda suke so shima yana karawa miya gishiri.
- Saboda haka ni – Madugun canji – a ra'ayina abar yan asalin yankin Darfur su sasanta tsakaninsu, idan akabawa al'ummar kasarSudandama zasu iya sasanta wannan rikici, batare da shishshigin wasu kasasheba.
- Akwai masu ra'ayin cewa kasar Sin da kuma Amurka ke hura wutar rikicin naDarfurdomin kowace daya daga cinsu na bukatar kwasas man petur da allah ya horewa yankin .. kenan kasashan mulkin mallaka ke kara wuta?
- Wannan dayane daga cikin dalilan da yasa rikicin yaki ci yaki cinyewa.
- Idan har wannan ra'ayi ya tabbata to manyan kasashe ke da alhakin cigaban matsalar .. to wane yunkuri ya kamata muyi domin dakatar da zubar da jinni?
- Kuma idan har wannan ra'ayi ya tabbata to banga dalilin da zai sa mu aika dakarunmu wannan yankiba.
- Wani dan jarida daga cikin mahalarta wannan huduba ya kada baki yace: Madugun canji, masu sauraron gidan rediyo da kuma talabijin din B.B.C. suna so mutabo wani bangare daban kuma.
Sabuwar tambaya : Madugun canji.
Akoda yaushe muna surutun sasanta rikicin Yahudawa da kuma yan Palasdinu .. tambayata itace : tayaya kake ganin za'a sami nasarar sasanta wannan rikici?
Madugun canji : Na gode da wannan tambaya taka, wannan rikici
yana da dogon tarihi, yayikamada jikin da rashin lafiya ya kwakuleshi.
Matsalar palasdinawa ita ta sanya gaba a tsakanin Larabawa da kasar Amurka, saboda nuna goyan bayan Isra'ila da take yi, bugu da kari kuma manyan kasashe basu damuba wajan ganin an warware wannan rikici.
Akwai wani tsohon shugaban kasar Italia da ya taba cewa : muna neman hanyar kwantar da wannan rikicine a yanzu, bayan shekaru masu zuwa kuma idan ya tashi to ba ruwanmu, sai suje can su karata.
Akwai hatsari a tattare da rannan magana, kamar misalin likita ne wanda ke bawa maras lafiya magani domin cuta ta lafa ba domin ya warke ba.
Wasu kuma na neman hanyar kwantar da wannan rikici ne domin dalilan kasuwancin su, ko kuam tsaron kasashen su.
Yayin da wasu shugabannin kanyi ruwa da tsaki wajan warware wannan rikici domin ace su mutanan kirkine, tayadda zasu cigaba da zama bisa kujerar mulki.
Wasu shugabannin kumakanshiga adama da su badan komaiba saidai domin yardar Amerika da Isra'ila, wasu kuma domin tsoron kada al'mmar kasashansu suyi masu bori tare da tsigesu bisa kujerar mulki.
Misali anan shine Shugaban kasar Amurka mai ci ayanzu, yana fatan ganin warware rikicin gabas ta tsakiyane domin asake zabarshi a matsyin shugaban Amurka karo na biyo.
Kenan kokarin da yakeyi saboda jam'iyyarshi ce ba saboda Isra'ila ko Plasdinu ba, wannan itace matsalar manyan masu fada aji.
Ni ban cikin wadancan mutane da na lissafa .. bani dogaro ga Amerika ko Isra'ila ko Plasdinu ko kuma Larabawa da dai sauransu .. ban bukatar su zabe ni, bani karkashin wata jam'iyyar siyasa,.
Bayan na yi nazari bisa wannan matsala sai na rubuta wanni littafi farinlittafi da ake kira ( Kitabul – Abyad ) a larabce, na kuma bashi taken ( Isradin ) anan ina nufin Isra'ila da kuma Palasdinu .. wannan littafi yayi bayani ra'ayoyin Palasdinawa da kuma Isra'ilawa yadda kowane bangaran ke ganin hanyar da ta kamata abi domin warware rikicin gabas ta tsakiya.
Hanya guda daya ta rage na sasanta wannan matsala itace Palasdinawa da kuma Isra'ilawa su hadu su kafa kasa daya mai bin tsarin mulkin Demokuradiyya a tsakaninsu, majalisar dinkin duniya ta jagoranci shirya zabe, idan Ba'isra'ile ko Bapalasdine ya ci zabe a bashi damar shugabantar bangarorin biyu, batare da nuna kabilanci ko kuma san kai ba.
Larabawa da Yahudawa asalinsu guda ne, dukkanninsu yayan Sam ne ..
Yahudawa an tsanesu ana korarsu a ko'ina cikin duniyarnan, tunda dai sun zabi rayuwa a wannan yanki namu to dolansune su zauna da mu lafiya batare da takalar fada ba .. Amerika bazata iya basu kariyaba har'abada, saboda haka ya zamo wajibi su nemi zaman lafiya dam u.
Batun da suke yin a ganin sun kafa kasar Isra'ila su kadai bazata taba yiwuwaba, kamar misalign mutumin day a shiga cikin teku ne da kasa a hannin shi bashi so kasar ta jike, kaga wannan mafarkine yake.
Kasar da suke cewa tasuce tana tsakiyar kasashan Larabawa ne, to gayamin ya za'ayi su kafata? A cikin kasar tasu akwai kimanin Larabawa milyan daya, ana sa ran cewa adadinsu zai karu ya zuwa milyan uku nan gaba.
Suna kuma cewa zasu bawa Plasdinawa damar kafa tasu kasar a Yammacin koginJordan, alhali kilo mita goma sha hudune rak tsakanin wancan kogi da Isra'ila, saboda haka cikin sauki za'a raba isra'ila gida biyu idan yaki ya barke.
Wadanda suka kafa kasar Isra'ila sun san da haka, su da kansu sunce kuskurene suka yi a shekarun 48.
Wannan shine dalilan da kasashen Larabawa suka ki amincewa da kasar ta Isra'ila.
Misali anan shine kasar Saipuros (Cyprus) wacce kasar Taki ( Turkey) ta amince da ita a zaman kasa, sauran kasashen duniya basu amince da ita ba.
Adadin Yahudawa a duniya milyan 12 ne kawai, idan akace wannan adadi nasu zasu komo Isra'ila, su kuma palasdinawa da suke gudun hijra a kasashan duniya sunkai mutane milyan biyar, ba zaiyiwu su rayu a yar kasar da aka yanka masu ba.
Tambaya ta gaba : Madugun canji mai zakace game da alakar jakadanci da kasashan Masar da kumaJordansuka kulla da Isra'ila … tsohon shugaba Yasir Afarafat shima ya kulla alakar jakadanci da Isra'ila, mai zai hana kasarLibyata kulla alaka da Isra'ila?
Madugun canji : kulla alaka ba itace matsala ba, matsalar mu itace yaya zamu warware wannan rikici.
Idan aka sami nasarar warware wannan rikici sai mu fara tunanin kulla alaka.
Na gode maku da wannan dama da malamai da kuma kungiyoyin daliban jami'arOxfordsuka bani.
Ashirye nake koda yaushe na gabatar maku da huduba a duk lokacin da na sami lokai.
Wata tambaya daban kuma : wace shawara zaka bawa mahukunta a kasashanIranda kuma Amurka na ganin sun bi hanyoyin lumana na sasanta matsalarsu?
Madugun canji : banga dalilin da zai sa su hana kasarIranamfani da fusahar no-kilya ( Nuclear ) ta tsaftatarciyar hanya ba.
Iadan kuwa Iran ta na so ta yi amfani domin kera makamin kare dangi ne to akwai ra'ayi biyu, na farko Iran tana iya cewa bazata fasa yunkurin mallakar makaman na kare dangu ba har sai sauran kasashen duniya masu irin wannan makami sun lalata nasu.
Na gode muku.
Wani dan jaridan B.B.C. ya kada baki yace : madugun canji ina so nayi amfani da yawun mahalarta wannan taro a jami'arOxfordna nuna godiyar mu ga wannan huduba taka.