Bookmark and Share

HIRAR MADUGUN CANJI TA SIYASSA WADA YAYI DA TALIBAYE DA MALLAMAN BABAR MAKARANTAR CAMBRIDGE


Al Gaddafi na hira Hausa

Image description

Muammar Al Gaddafi na hira Hausa

Muammar Al Gaddafi speaks Hausa 

Audio |  |

Video |  | 

Image description

HIRAR MADUGUN CANJI TA SIYASSA WADA YAYI DA TALIBAYE DA MALLAMAN BABAR MAKARANTAR CAMBRIDGE 

22.10.2007

Bismillahi :


Na farko daye ina gayda mallamaye da Taliban wanan makarantar taCambridge. Kuma ina gayda ku game da gayatar da kuka yi mini domin in yi hira da ku . Na samu irin wanan gayatar yaw hiye da watani daga makarantarOxfordinda na yi hira da su bisa tawrarun dan adam . A yaw kuma ina murna game da hirar da za ni yi da ku bisa tawrarun dan adam . Ina farin ciki koreye idan ina ganin mayan makarantu kamar naOxfordko kuma naCambridgena kula da lamuran da duniya ke ciki . Yaw daye akoye wasu lamura dake da tassiri ga rayuwar mu duka inda muke . Yaw babu shaka duniya ta dawki hanyar zama unguwa guda kamar yada ake cewa . Sabili da haka ne ya kamata wanan unguwar ta kula da kanta musaman ma domin rayuwa a cikin zaman lahiya da kwanciyar hankali dan wanan unguwar ita kadaye ce . Idan mun dubi giragizan dake kumshe da tawraru zamu ganin cewa giragizan dake da rana kadan koreye kuma a cikin wa-anan giragizan ne dan adam ke rayuwa . Kuma a koye mamaki koreye game da cewa duka da haka yan adam ne ke ta yake-yake tsakanin su . Kuma gayatar da kuka yi mini domin hira da ku na nuna da cewa yaw muna da bukatar juna domin warware wasu matsalolin da duniya baki daya ke fuskanta . Kuma yaw yaduwar fusa’a ya kawo sawki a cikin komi . 


Bayan haka kuma inabakusanin cewa a ranar 27 na wanan watan a koye wani zaman taro na kasa da kasa a garin sirte game da warware matsalar yankinDarfur..  


Aman ina gaya muku inada ra’ayi na na musaman game da matsalar da yankin Darfur ke fuskanta domin gobe zaku zama mayan jami’an kasashen ku kuma ya wajaba a issar da wanan nazarin zuwa gare ku da yan kafofin labaru da duka mahalarta taron sirte wanda za a yi a ranar 27 na wanan watan idan Allah ya kaymu . Kuma wanan lamarin yanakamada lamura da dama dake faruwa a cikin nahiyar afrika kamar matsalar kabilanci .  Yala kuma zaku mamaki idan na ce muku mafarin wanan matsalar ya huto ne daga fadakanrakumi da ta zama yaw matsalar kasa da kasa . Nahiyar afrika daye na kumshe ne da kabiloli da dama da suka yadu a cikin kasashe da dama bayan da aka raba wanan nahiyar a kasashe hiye da 50 .. 


A takaice daye wa-anan matsalolin ba zasu karewa ba a afrika domin al’umomin ta na fuskantar ta ne yaw hiye da darurruwan shekaru . Aman kuma ina cewa wa-anan matsalolon zasu karewa idan al’umomin ta sun samu wayewar da ya kamata . Aman baton da muka fada ciki shi ne har mun rigaye mun siyassar da wanan matsalar taDarfurdomin ta zama matsalar kasa da kasa duka da cewa akoye irin wa-anan matsalolin da an kashe wutar wasu ba tare ba da mun sani . Yaw daye mayan kasashen duniya na zura hanuwan su a cikin duka yankin dake da arzikin man petr kuma wanan shi ya sa matsalar ta zama matsalar kasa da kasa . Babu shaka mayan kasashe ne ke bayan abin dake faruwa a yankinDarfur.. Ina tsamanin cewabakutaba jin wanan maganar ba duka da cewa ta na da muhinmanci koreye gare ku . Ina ce muku ina daye daga mutanen da suka san nahiyar afrika da kyaw domin nayi balagoro da mota inda na yi kilometer dubu ishirin a cikin afrika inda na ga yada al’umomin ta ke rayuwa daga makiyayan su har manoma har na cikin kawyuyuka da garuruwa da abincin su da ruwan da suke sha ..Kuma ina daye daga wa-anda suka ga lokacin mayan yan gogormayar ta kamar Jomo Kenyeta da Jamal Abdul Nasser da Hile Selasie . Kuma baye kamata ba ana siyassar da matsalolin da afrika ke fuskanta domin duka matsalolin ta na da alaka da kabilanci . 


Matsalar da yankinDarfurke fuskanta bata da alaka da siyassa ko zamantakewa ko tatalin arziki ..matsala ce tsakanin kabilu ..Sawren su makiyaya ne wasu kuma manoma ne kuma fadace-fadace tsakanin su akoye su a ko wane wuri na duniya . Aman da wanan matsalar ta kare inda akoye shiga tsakani . 


A cikin kasa guda ta afrika ana samun kabilu da dama kuma ko wace kabila na da sarakunan ta al’adun ta kamar kasarSudan. Wanan kuma shi ne tsarin mu a nahiyar afrika kuma inda an bar ma sarakunan yankinDarfurwanan matsalar da ko sun warware ta tun ba yaw . Aman idan sojoji musaman ma na kasashen waje sun stunduma wata jiha bata da kuma karfin warware wanan matsalar . Kuma saye ku ga talakawa aDarfurko kuma ko wane wuri na murna game da taimakon da ake kaymusu bayan sun kirkiro matsalar da ta kaye su ga haka . Aman kuma basu san ba da wanan taimakon  ba na jinkaye bane domin yana kambacin wutar da ake kara hurawa . 


Saye ku ga mutane sun turke kanun su a cikin wani wuri da suke maydawa na yan gudun hijira kuma suna jiran taimako . To ina ce muku irin wa-anan mutanen basu fatan matsalar Darfurta kare domin hanya ce ta karbar taimakon jinkaye daga kungiyoyin kasa da kasa . Bayan haka kuma saye ga wani magajin gari ko kuma mallamin makaranta ko kuma jami’in soji ya samu gayata daga kafofin watsa labaru na duniya game da wata matsala kamar taDarfursaye ya fara magana da sunan kabilar shi ko kuma da sunan wasu mutane da ake zalumci .. Kuma irin wanan lamarin akoye shi a ko wane wuri na duniya musaman ma a cikin kasashen da aka yima mulkin malaka dake fama da rishin ci-gaba . 


Irin wanan mutun baye fatan matsala ta kare domin a cikin ne yake da kima kuma yana maganakantawrarun dan adam . Sabili da haka ne madugun canji ya bayana cewa baye kamata a siyassartar da irin wa-anan matsaloli dake kananan matsaloli a farko domin suna da alaka da kabilanci . Kuma duka kabilolin dake afrika na da sarakunan su dake warware duka matsalolin dake tsakanin kabilolin su idan ba a siyassartar da matsalar ba . 


Aka ce matsalarDarfurna da alaka da bambancin fata dake tsakanin wasu bulale da farare ko kuma tsakanin larabawa da afrikawa . To larabawa da kanun su afrikawa ne .. kuma na san mayan kabiloli kasar Soudan kamar kabilun Al Razikat da ta Zagawa da ta For . Kuma babu wanda ya iya ya sa bambanci tsakanin wa-anan kabilun dake magana da harshen larabci bayan haka kuma dukan su adinin su shi ne musulumci kuma babu wada bata jin yaren wata ba . Wa-anan kabilun sun cudu koreye tsakanin su al’amarin da ke sa akoye wuya koreye wajen bambanta su . Sabili da haka ba ka iya bambanta balarabe da wani iri da ba na larabawa ba . 


Bayan haka kuma gaskiya ce nikegayamuku domin abo ne dakekamada wassa kollon kafa tsakanin kasa da wata kasa inda kowa ke neman mahiya goyon baya . Sanan kuma akoye mayan kasashe dake hangen arzikin kasa da Allah ya hore ma wanan yankin saye su kawo sojojin su da niyar shiga tsakani  domin warware wanan matsalar . Al hali kwa ba shine ba abinda suka sama gaba kuma duka gurin su zuwa gare mu baye da kyaw . Ya kamata kuma mu gane da haka. Kuma tun lokaci daularRomaniahar zuwa ta Mongol ko kuma ta musulumci dukan su gurin da suke sun su cinma shine na ganin fadin kasashen da suke malaka ya kara gima a duniya .



Bayan haka na san da kuna sun hirakanmatsalar yankin gabasse ta tsakiya ko kuma in ce matsalar palastino . Diyana ina ce muku na san tarhin wanan yankin . Na farko daye ina ce muku palastinawa da israilawa diyan wa da kane ne . Kenan assulin su guda .. Domin dukan su sun huto ne da kaka guda wanda ke Sam .. Kuma ko harshen larabci da na yahudawa na kusa ga juna . Bayan haka kuma kasar da ake ce ma palastino  kasar palastinawa da israilawa ce .. Dukan su na da hakin rayuwa a ciki kuma babu wanda ke da hakin cewa wanan bangaren na shi ne har ya gina kasa a ciki da baye rabata da kowa . Sabili da haka ne kuma larabawa suka ki yarda da abinda ake cema israila dan kawaye sun yi shelar girka kasar su . Wanan shi ne ya kawo matsalar kin yardar larabawa  ga abinda ake cema israila . Kamar lokacin da kasarCyprusta yi shelar kafa kasar ta . Babu kasar da ta kawo mata goyon baya imba kasar Taki ba kuma ba dan  wani abo ba dan daye kawaye kasashenCyprusna Taki da na Girka duka assulin su guda . Kuma daka da yaw babu wanda ya yarda da wanan kasar taCyprusaman baye hana ba an yarda da abinda ake cema israila .. Kuma baye kamata ba a yarda da wata kasa yayin da ake kawo ma wata goyon baya . Game da matsalar palastino tun shekara ta 1948 ne aka yi baban bato domin tun wanan lokacin ne aka yi shelar kasar israila akankasar da ake jayaya a kanta . Idan an bar tarihi ganga ina ganin cewa yaw da wuya a samu zaren warware matsalar palastino domin an mayda ta kamar taDarfur.. Domin kowa na anfani da ita domin cinma gurin shi .


 A lokacin da akoye kungiyar hadadiyar kasashen Rasha da kungiyar neto kowa daga cikin su yayi anfani da wanan matsalar  domin hakaka gurin shi .. Duka da masu mutuwa sune palastinawa da israilawa . Kuma duka fadin kasar dake tsakanin kogin Jodan da teku baye wuce kilometer 15 ba da kuma dimbin mutane . Kenan ta yaya ne za a kafa kasa a cikin irin wanan wuri .  Kuma idan palastinawa sun kafa kasa duka garuruwan dake cikin wanan yankin zasu zama kalkashin ta musaman ma Tel-Aviv . Idan aka yi yaki kenan za a raba wanan kasar a biyu bangare guda na cikin yankin mediteranea yayin da sawren bangaren na cikin  kogin jodan . A halin yanzu akoye kimanin mutun million guda a cikin abin da ake cema palastino kuma adadin su na   ta karuwa a ko wane lokaci .  Bayan haka kuma akoye kimanin palastinawa million guda a cikin abinda ake cema israila . Suma adadin su na ta karuwa . Kenan har yanzu ba yahudawa bane kawaye ke cikin abinda ake cema israila domin akoye palastinawa million guda a cikin ta . Kuma kun san da adadin palastinawa ya fi na israilawa karuwa da sawri . Palastinawan dake cikin abinda ake cema israila na zamne lami lafiya da yahudawa .. To wanan shine missali na kasar da ya kamace su dukan su . Ina nufin su girka kasa guda da zasu sama sunan isratine ko palastino ko duka sunan da suke so . 


Yaw matsalolin dake faruwa tsakanin palastinawa da israilawa na futowa ne daga wa-anda ke rayuwa ba cikin abinda ake cema israila ba . Ya kamata al’umar kasa da kasa ta kafa ma duka bangaren da tatalin bunkassa bambanci adini ko na iri dokoki masu karfi da zaye hana wanan bangaren ya ingantar da abinda yake so . Kuma kasar da palastinawa da israilawa ke fada a kanta karama ce koreye ba a iya girka kasashe2 akanta . Kenan kasa guda ta demokradiya ita ce zasu iya girkawa idan suna sun zamna lami lafiya . Kuma kun san da a lokacin da aka kori larabawa da yahudawa daga garin Andalus a karni na15 kasashen larabawa ne suka karbi yahudawa bayan haka kuma suka kare su . Sanan kuma ko lokacin da romaniawa suka ragargazarda garin al qods a shekara ta 72 kuma suka kori yahudawa har wayaw larabawa ne suka karbi yahudawa . Kenan wanan na nuna da cewa larabawa sun yi zaman kare yahudawa . Kuma kun san da larabawa da yahudawa yan wa da kane suke domin annabi Ibrahima na da diya 2 guda Ismaila wanda larabawa suka huto daga gare shi da Ishaka wanda ke kakan yahudawa dake mahayfin Yacuba maye suna israila . To wanan sunan shine yahudawa suka sama kasar su . Wanan matsalar da wa-anan al’umomin suka samu ta huto ne daga mayan kasashe dake samun anfani irin wanan lamarin tashin hankali . 


Kenan ya kamata palastinawa da israilawa su koma rayuwa a cikin kasa guda . Na rubuta littafi maye suna isratine da ya hada sunayen israila da palastino .. Ya kamata a ce kuna da irin shi da aka fasara a harshen turanci .. Wanan littafin na gayatar girka kasa guda ta demokradiya tsakanin al’umomin israila da palastino .. Sun iya su gudanarda zaben shugabancin kasar kalkashin jagorancin majalisar dimkin duniya .. Shugaba guda ne zasu zabe bapalastine ne ko bayahude ..Kuma akoye ma irin wanan missalin a cikin abinda ake cema israila domin akoye jam’iyar siyassa ta larabawa  kamar yada akoye larabawa dake mambobin a cikin majalisar dokoki Knesset ta yahudawa . Kuma ya kamata ku san da akoye cudaya koreye tsakanin palastinawa da israilawa musaman ma a yankin kogin jodan da ziringaza. Bayan haka kuma palastinawa ne ke ayki a cikin kampanonin kere-kere na israilawa . Duka wanan na nuna alakar dake tsakanin su . Sabili da haka kuma ina kira domin komowar yan gudun hijirar palastino da aka kora tun shekarun 1948 da 1967 su komo gidajen su . Bayan haka kuma baye kamata a samu makaman kare dangi a cikin kasar palastino koma Yasser Arafat ko kuma Mahmud Abbas ne ke jagorancin ta . Ina gayatar ku domin karatun littafin da na rubuta maye suna isratine .



Bayan haka kuma zamu tantamnawakansake tsara ofishin majalisar dimkin duniya . Tun ba yaw bane muke zancekanmambobin wanan ofishin dake ta karuwa da mambobin ta na dundundun da wa-anda ba na dundundun ba . Kuma majalisar dimkin duniya  ba ita ce ba majalisar tsaro .. Domin majalisar dimkin duniya na kumshe ne da ofishoshi da dama a cikin ta kamar su kotun kasa da kasa da UNESCO da UNICEF da FAO . Aman kuma abinda ke faruwa a yanzu babu adalci da demokradiya a ciki . Sabili da haka kuma ya kamata irin wanan lamarin ya kare . A takaice daye ikon danniya da ta’adanci ne kawaye ke faruwa a cikin ofishin majalisar dimkin duniya domin kasashen dake da hakin veto ko kuma na dundundun sune ke abinda suka dama . Sabili da haka ne kananan kasashe da massana kamar ku ke kin yarda da abinda ke faruwa a cikin majlisar dimkin duniya . Kuma yaw yake-yaken dake faruwa a cikin kasashen Iraki da Afghanitan daYugoslavia  na faruwa ne da sanin ofishin majalisar dimkin duniya da majalisar tsaro ta kasa da kasa . To danmi nene a lokacin da kasashen amuruka daBritainsuka yaki kasar Iraki majalisar tsaro bata yi ayki ba da kudurin ta lamba na 7 .. 


Wanan na nuna cewa wa-anan kasashen na da hakin rushe ko wane kudurin da basu yarda da shi ba . Idan kuma haka lamarin yake to ina ganin majalisar tsaro ta fita daga ta kasa da kasa dan ta koma ta abukan juna .. Mun yi kira domin sake tsara majalisar dimkin duniya domin ayi ayki da demokradiya a cikin ta .. Kuma mun dawki wanan ofishin a matsayin majalisar dokokin duniya ko kuma abinda ake iya cema international assembly inda ofishin ke gabatar da ra’ayin mutanen dake mambobi a cikin ta . 


Hal kuna ganin cewa gomnatin kasarBritainna iya hudo da kudurori kuma ta gayaci majalisar dokoki domin zartar da su ? Baye iyawa. Majalisar dokoki ita ce ke hudo da kudurorin da gomnati ke ayki da su . Abin dake faruwa a cikin ofishin majalisar dimkin duniya shi ne kamar gomnati ne ke dawkar kudurorin da majalisar dokoki ke zartar da su . Kenan kamar an sa doki gaba ga amalinke . Majalisar dimkin duniya dake kumshe da duka kasashen dake mambobi a cikin ta ita ce kawaye ke da izinin hudo da kuduri kamar kafa ma wata kasa takunkumi ko kuma  wata doka . Kuma idan majalisar dimkin duniya ta hudo da wanan kudurinkanwanan kasar ya kamata ta yarda da shi domin duka al’umomin duniya ne suka dawki wanan kudurin . 


Aman saye ka ga kasa guda ko biyu sun  hudo da kuduri da suke cilasta ma kasashen 14 da ake cema majalisar tsaro wanan ba adalci bane . Kuma ya kamata irin wanan lamarin ya kare . Sake tsara ofishin majalisar dimkin duniya na nufin majalisar tsaro ta gabatar da ikon ta ga baban ofishin . Kuma ya kamata ofishin yayi ayki da kudurin shi lamba na 7 da duka kudurorin da take dawka domin ya kamata majalisar tsaro ta kasa da kasa ta yi ayki da duka kudurorin da ofishin majalisar dimkin duniya ke dawka idan ana sun sake tsara wanan ofishin . Idan lamuran ofishin na tafiya kamar yada suke a halin yanzu to wasu kasashe zasu fita daga ciki domin su girka wani ofishi daban na kasashen da basu ji dadi ba . Kundin ofishin majalisar dimkin duniya ya hana ayi anfani da karfi koda bada tsorokanwata al’uma . Aman yaw kowa na ji yana gani yada wasu ke anfani da wanan karfin .. Kenan wanan kundin yak aye karshen shi . Bayan haka kuma akoye wasu tsofin matsaloli dake tsakanin ofishin da kasashenLibyakoPanamakoYugoslaviako Iraki koAfghanistan.. Wa-anan matsalolin sun zama suma kundi ta hanyar baki .. 


Kuma yaw abinda muke so shi ne aba kudurori matsayin da ya kamace su domin mun yi la’akari da cewa yaw karfin damtse ya fi kudurori karfi . 


Dukan mu mun san da yaw babu wata babar kasa dake magana da gaskekankare hakin bil adama da demokradiya . Kenan kamar yada nagayamuku ne tun farko . Ya kamata a gabatar da demokradiya a cikin majalisar dimkin duniya . Game da demokradiya a cikin koren littafi ina ganin kun karanta abinda take nufi a cikin harshen turanci .. Dake ba ra’ayi na ba kawaye .. Na gangama tarihin da duniya ta jaraba bayan haka kuma na san matsalolin cikin gida da na waje da matsalolin al’umomi da farin cikin su da halin yaki da na zaman lahiya.Kalmardemokradiya daye  na kumshe ne da wasu kalmomi biyu na larabci dake demos wanda ke nufin al’uma da kracy dake nufin kujeru . Kenan demokradiya na nufin al’umar dake zamakankujeru . 


Wanan Kalmar ta larabci ce domin ma ana samun ta a cikin ko wane harshe . Idan kuma muna sun mu yi ayki da ita to ya kamata mu bar al’uma ta zamnakankujeru .. domin al’uma ce kawaye ke da izinin kirkiro tsari ko kuma ta dawki kudurorin da ya kamace ta dan baye kamata ba a bar iko a cikin hanun wasu mutane kalilan da ake cema gomnati ko kuma abinda ake ma wakilaye . Tsarin wakilci shi ne ya bada al’umomi . Baye kamata ba a wakilci al’uma domin tana nan ..Kuma wakilci dujalanci ne ..Kenan al’uma ce ke kawaye ta issa tayi ikon kanta da kanta domin harakokin siyassa da tatalin arziki da zamantakewa al’uma ce ke tsara su a kaye tsaye .. Ta yaya za a iya dawkar mutun guda domin ya wakilci mutane million guda ko kuma mutane kalilan su wakilci milliyoyin mutane .. 


Aye wanan ba gaskiya ba ce . Wa ke ce muna mutumen dake magana da sunan dubanin mutane ya iya ya gayi abinda suke so .. Irin wanan mutun na magana ne da sunan shi ne kawaye  domin kuna ganin wakilaye a kasar Britain na dawkar kudurori ko kuma suna goyon bayan wata siyassa aman baye hana mutane su huto a cikin hanyoyi dan yin zanga-zanga . Inda wakilan na yin abinda al’uma ke so danmi za a zanga-zanga ? Wanan ya faru a kasar amuruka inda al’uma ta yi Allah wadai da yakin da aka kayma kasar Iraki aman majalisar dokoki kasar Amuruka ya kawo goyon bayan shi ga yakin .. Kenan majalisar dokoki bata yi wakilcin al’uma ba . A halin yanzu ma al’umar kasar Amuruka na fatan dakarun ta su fita daga kasar iraki aman gomnati baye yarda ba kuma majalisar dokokin kasar Amuruka bata dawki mataki ko guda . Kenan al’uma na bangare guda a lokacin da majalisar wakilaye ita ma na bangaren ta . Demokradiya a cikin koren littafi na nufin ikon al’uma .. 


Ikon al’uma kuma shi ne komitocin jama’a inda duka dan kasa da ya balaga namiji ko mace ke da izinin kawo ta shi gudun mawa a cikin tafiyar da harakokin kasa . Yanzu idan an raba al’umar kasarLibyaa cikin kominaye dubu 30 ..kuma ko wace komona na kumshe da mutun 100 maza da mata da duka adadin sun a kaye million 3 ..wa-anan million 3 su ke da hakin gabatar da iko a kasarLibyadomin sawran yara ne da tsofin da daye wa-anda basu iya gabatar da iko . Kenan mutanen da zasu iya gabatar da iko basu wuce million 3 ba kuma su ne ke tsara ajendar aykin su da siyassar su ta cikin gida da ta waje har tsawon shekara guda . bayan haka kuma su sake gamuwa a shekara ta gaba . Ina nufin “babu demokradiya saye da taron jama’a” .. “Kuma taro da komitocin jama’a na a ko ina “ .. Wa-anan sune take na gaske . Ina ganin kuma bisakanwa-anan lamuran ne kuka gayace ne domin tantamnawa akansu . Kuma ina fatan mu ci gaba da saduwa da juna musaman ma idan ina da lokaci . 

 A yanzu kuma ina jiran tambayoyin ku .

Tambaya ta farko ta zo ne daga baban massani falsafa mallam Michael  da ya ce ya na gayda madugun canji kuma yana matukar farin ciki game da jagorantar talibaye 15 na babar  wanan makarantar ta Cambrige a bukukuwan da aka gudanar a watanin February da march na wanan shekarar a kasar ku .. Inda kuma muka tantamnakanalakar hulda ta kasarLibya.. Bayan haka kuma na mayda hankalikanbinciken da na yi game da shekaru na 1990 da shekarun yanzu da kuma karfafar da alaka tsakanin kasashenLibyada Amuruka . A lokacin da mataimakin shugaban kasar Amuruka mallam Dick Cheney ya bayana cewa sun kada mulkin Saddam Hussein Kuma yaw Saddam na gidan yari . Madugu Al Gaddafi na kasarLibyaya huto bayan kwanaki 5 da haka ya bayana cewa : zasubarikera makaman kare dangi .. Kuma dan ku Saiful Islam ya ji abinda kuka gayi .

A wanan lokacinLibyata yi baban batokanamuruka .. Kuma wanan na nuna durkusar da ta yi a panin siyassa .. Aman kuma yanzuLibya  na da kwanciyar hankali game da abubuwan da take yi .. Ina tambayar ku madugukanabinda ya kawo cawtatar da alaka tsakanin kasashen amuruka daLibya  :


-          Madugu :


Na gode docta Michael .. Kuma ina gode maka da halartar ka bukukuwan al’umar kasarLibya. Ka san idan wani abo ya faru a cikin duniya kowa ma na sun yayi anfani da shi kuma babu wanda zaye gayin wani abokanwani lamarin dab aye faru ba .. Ina nufin danmi Cheney baye gayi wanan maganar ba kaminLibyata dawki wanan matsayin na tarihi ? Danmi baye ce ba zamu saLibyata bar da karfi a cikin watani 5 tsarin ta na kera makaman kare dangi  ? Dan mun yi kaza da kaza a kasar Iraki .. Aye ko shugaban kasar amuruka dakanshi ya yarda da cewa yarjejenia tsakanin kasashen 2 da ofishin kasa da kasa dake kula da kera makamashin nuklea  sun kaye tsawon watani 9 kamin mu kaye ga natijar barin kera makaman kare dangi . A wanan lokacin ba a ko kaye ma kasar iraki hari ba bale a kada ikon Saddam Hussein . Inda muna tsoro danmi ne muka ci-gaba da kafa kampanonin kera makaman kare dangi ko lokacin da mahawkci Reaggean ke ikon amuruka duka da mungayamusu cewa mahawkci basu yarda ba saye da likitoci suka tabatar da cewa ya fama da ciwon Azelmeiher . 


Ina ganin ba tsoro bane ya sa muka bar shirin mu na kera makaman kare dangi da ya zama a wani lokaci abin zamani da kowa ma ke fatan samun shi. Mun bar shi bayan da muka imani da cewa baye da anfani kuma bayan haka an gano da shi domin an ma cabke wasu kayan kera su . Bayan haka mun tantamna tsakanin mu da Amuruka daBritainmusaman ma aboki na Blair da wasu massananLibyada na kasa da kasa na wanan panin .. Mun ga da cewa akoye wuya wanan shirin ya tabata bayan haka kuma mun ga da cewa zaye kalafa muna kudi da dama  . Kuma danmi ma ne zamu kera makamin kare dangi ? Yala akoye maye cewa wallahi zamu kera shi domin mu jefa shikanisraila . Wanan kuma ba gaskiya ba ce domin kamar yada nagayamuku ne tun da farko a cikin abinda ake cema israila a koye kimanin palastinawa million guda .Libyabata iya jefa bum din nucleakanabinda ake cema israila alhali akoye million guda na palastinawa da million 3 na yahudawa .. Kuma tun yankin kogin jodan har zirin gaza har kasashen Siriya da Leabanon da Jodan da Masar babu wada zata hita daga mugun tassirin irin wanan makamin na nuklea . Kenan tun daga nan mun iya mu gane da cewaLibyabata da bukatar irin wanan makamin na nuklea . Kuma koma idan an ce kasarLibyazata jefa ma nahiyar turai wanan makamin .. 


Yaw daye kasashen turai basu bane suka yi zaman mulkin malaka .. Yaw nahiyar turai na da cawcawar alaka da nahiyar afrika musaman makankasuwanci da zuba jari da kare yanayi da tekun mediteranea da duka wasu ayukan bunkassa tatalin arziki . Kuma a nahiyar turaiLibyana abukaye da dama . Kenan babu sabilin kera makamin nuklea a wanan bangaren . kuma halLibyazata kera wanan makamin ne domin ta jefa ma kasar amuruka shi? Kuma anan maLibyana da bukatar goyon bayan wasu kasashe da zata karewa game da tassirin wanan makamin wanan kuma na da wuya koreye ga kasa kamarLibya.Libyabata iya jefa ma amuruka makamin nuklea domin amuruka zata mayda mata da dubanin irin wa-anan makaman . Ina ganin mahawkaci ne kawaye ke iya tunanin ya jefa ma kasashe kamar amuruka ko Rasha koChinamakamin nuklea domin suna da dubanin irin wa-anan makaman . Kuma ba a afrika bane zamu jefa wanan makamin ko da mun kera shi . 


A afrika kuma munakanhanyar gina nahiyar mu da kadan kadan . A yanzu daye zance kera makamin nuklea ya kare kuma a wani lokacin mun so mu yi shi domin yana abin zamani . A wanan lokacin mun ga kasashenPakistandaindiasun kera wanan makamin dan kowa cikin su ya karekanshi ga  wacen kasa . Makaman kare dangi mugan makamaye ne sabili da haka ne muke kira ga yada irin wanan shirin a ko wace kasa ta duniya . Kuma a Libya Allah kadaye ne muke tsoro ba mutun ba .. 


Kuma duka abubuwan da Dick Cheney ya gayi ko kuma Reaggean wanan ya zama batun su . Kuma ina fatan Cheney ba marashi lafiya bane kamar Reaggean . Bayan haka kuma ina yima Cheney fatan koshin lafiya domin na ji an fasa shi har so 5 ga zucia . Kuma ya kamata ku san da koma karamar kasa kamarLibyata janye kanta daga yakin kasa kamar amuruka dake da dubanin makaman nuklea da na kare dangi . Aye wanan ma yana cikin hikima da kuzari . Na ce wanan yana cikin hikima da kuzari domin mune muka ga dama kuma muka babu anfani ga kera makamin nuklea . Babu wanda ya cilasta mu ga haka .

Tambaya : Madugu kuna da niyar karfafar da kungiyar tarayyar afrika da girka daular afrika .. Hal kuna ganin cewa wanan lamarin zaye tabata nan da zuwa shekaru 10 na gaba?


Madugu :  Ina gode maka da wanan tambayar .. Ya iya tabata imba dan da? Na farko daye a nahiyar afrika mun bi abinda turawa ke yi ..kuma nahiyar turai na kumshe  ne al’umomi da dama .. Kun san da tun wani lokaci da baye dade ba al’umomi sun yi zaman yakin juna a baban yaki na farko na duniya ko kuma a na 2 ko kuma yakin shekaru 30 ko na shekaru 7 ..inda dubanin mutane suka rasa rayukan su . Kuma duka da wa-anan yake- yaken da suka faru a nahiyar turai baye hana ba yaw turawa sun ga muhinmancin hada kanun su . Kuma muma a afrika mun ga da wanan ra’ayin na da kyaw koreye . Sabili da haka ne muka bishi . Al’umomin afrika basu yaki juna ba .. kuma afrikawa al’uma guda ce a cikin nahiya guda.. duka da cewa akoye kimanin kabilu 1000..Baye hana ba muka hada kanun mu . Kuma ko lawnin afrikawa ya bambanta da sawran lawnin fatan sawran al’umomi .. Kuma yaw sabon salon da duniya ke ciki baye barin wata kasa ta kalubalanci wasu matsalolin wanan zamanin . Idan kasashe kamar Jamus koBritainko Faransa ko Italia basu iya rayuwa saye cikin tarayyar turai ta yaya za a iya tsamanin kananan kasashen afrika su rayu dakansu . Kasashen afrika basu iya rayuwa saye a cikin hadin kanun su .. Kuma lokacin da hadinkannahiyar afrika zaye tabata ko kuma gina daular afrika wanan lamarin na cikin hanun afrikawa ..


Tambaya : Madugu muna gode muku da bamu lokacin ku .. Kuma wanan tambayar ta huto ne daga bangaren hausa na rediyon BBC na kasarBritain. A yanzu daye hadinkannahiyar afrika al’amari ne da zaye tabata . Bayan haka kuma mun yi imani da hadinkankasashen larabawa ..Kuma muna gode ma kuzarin ku game da hadinkanafrikawa .

Madugu :  Ina ganin tambaya ka nakamada ra’ayi da ka baza .. Game da hadinkanlarabawa in ace muku duniya ta yi zaman rayuwa a cikin taron adinai da iri guda . An yi zaman lokacin kasar islamiya ko ta romaniawa ko ta usmaniawa ko ta abbasiawa …


A lokacin gina daular dake da alaka da iri an gina kasashe kamar Italia da Taki da China ..Aman duka wanan zamanin ya wucekanlarabawa da basu yi komi ba domin hada kanun su . Yaw kuma bayann da duniya ta shiga wani sabon salo akoye wuya kasa kamarLibyata hadakantad a Iraki ko kuma Siriya ta hada kanta da Marrakush ..Duka da cewa Libya da Marrakush dukan sun a cikin afrika . Kenan suna iya hada kanun su . 


Kuma yaw kasashenasiana nan na hada kanun su a cikin sabuwar kungiyar Comonwealth da ta yi zama a cikin kasashen hadadiyar rasha .. kuma bayan haka akoye kungiyar tarayyar Afrika da kungiyar tarayyar turai .. da kasar Amuruka .. da kungiyar hadinkankasashen Amuruka ta kudu . Wanan na nuna da cewa duniya zata rabuwa a cikin mayan kasashe 7 ko 10 ko kuma kungiyoyi da zasu zama tamkar kasa . Kuma ko kudadaen kasashen na cikin hanyar bacewa domin su zama kudaden kungiyoyi 7 ko 10 da bankunan su . Wanan ita ce hanyar da duniya ta dawka nan da zuwa gaba .  yaw da wuya kayi zance kan hadin kan kasashen larabawa a cikin irin wa-anan kungiyoyin domin yaw da larabawa basu san a cikin wace babar kungiya ce zasu sa kanun su . Saye daye idan sun ji kiran da na yi musu bayan da na ziyarci kasashen larabawa da dama inda na gayace su ga shiga cikin kungiyar tarayyar afrika . A yaw kuma kimanin hiye da kashi 3 na larabawa dukan su afrikawa ne sawran kashi 3 kuma na cikin nahiyar asia da kogin larabawa da kogin sham .. Wanan kuma shi ne halin da duniya take ciki a yanzu .. Larabawa basu da wani hali saye hada kanun su da afrikawa .


Kuma maganar da duniya ke akanta yaw ita ce ta kafa mayan kungiyoyi da kare arzikin su .


Tambaya :


Madugu .. kun yi namijin kokari domin korar mulkinkamakarya da na daniya da kuma bunkassar da yan cin kaye dake da anfani ga kowa . Kamar yaya kuke gani abin dake faruwa a kasar Iraki musaman ma wanda Amuruka ke yi a cikin wanan kasar .

Madugu :  Ina ganin babu wanda ya iya ya san abin dake wakana a kasar Iraki domin ko yakin da aka kayma wanan kasar ya tabata ne ta hanyar bato kamar yada kasashen amuruka daBritainsuka yarda da shi . Sun ce akoye makaman kare dangi a kasar Iraki duka da sun ayka komitin bincike a wana kasar baye hana ba sayda suka kayma kasar Iraki hari bayan haka kuma suka gano cewa babu makaman da suke tsamani . Yaw sun ragargazarda kasa gudakankarya musaman ma idan mun san da mayan kasashe masu kujerar dundundun su neke irin wanan lamari da baye kamata ba . Kuma idan irin wanan lamari na faruwa sawran kasashen duniya basu iya samun kwanciyar hankali . Kuma idan kasashen da suka kayma Iraki hari na da niyar gyara baton su ya kamata ne su janye daga kasar Iraki dake kasar irakiawa.

Shugaban kungiyar Taliban babar makarantar Cambrige: Mun gode muku madugun canji game da halartar ku wanan taron .    

 

 

Bookmark and Share