ALBARKACIN
BUKUKUWAN SALLAR MAULIDIN MANZON ALLAH MUHAMMAD ( S.A.W. ) MADUGUN
CANJI YAYIWA SHUGABANNI DA KUMA JAMA'AR MUSULMAN DUNIYA LIMANCIN
SALLAH A BABBAN BIRNIN KASAR UGANDA
KAMPALA
Muammar Al Gaddafi na hira Hausa
Muammar Al Gaddafi speaks Hausa
ALBARKACIN BUKUKUWAN SALLAR MAULIDIN MANZON ALLAH MUHAMMAD ( S.A.W. ) MADUGUN CANJI YAYIWA SHUGABANNI DA KUMA JAMA'AR MUSULMAN DUNIYA LIMANCIN SALLAH A BABBAN BIRNIN KASAR UGANDA KAMPALA
15.03.2008
Da sunan Allah.
Yan uwa shugabanni wadanda kuka sami damar halartar wannan waje a wannan rana mai albarka : yan uwa musulmai daga nahiyoyin duniya baki daya, mun hadu yau a wannan wuri a birnin kampala domin mu gudanar da bukukuwan maulidin Annabi Muhammad (S.A.W.) hakkin al'ummo ne su gudanar da wannan biki, kasancewar Annabi Muhammad manzon Allah ne ya zuwa ilahirin bil'adama, kuma cika makon Annabawa, Musulumci shi ne kadai addinin da Allah ya yarda da shi, dukkannin manzanne da suka gabaci annabi Muhammad sun rayu ne bisa tafalkin Musulumci .. duk mutumin da yayi imani da Allah da kuma manzannin shi ya zamo musulmi, Annabi Muhammad ne ya zo a karshen su.
Allah (S.W.T.) ya kaddarawa yan adam da su kasance bisa kan addini guda akarshi wato addinin musulumci, shi ya sa ya aiko annabi Muhammad ga dukkannin bul'adam ba Kaman sauran annabawan da suka gabace shi ba, wadanda aka aiko su ya zuwa jama'ar su ko kuma kabilar su.
Allah madaukaki yace : ( Musulumci shi ne kaday addini a wajan Allah ) haka kuma y ace : ( Duk wanda ya zabi wani addini wanda ba musulumciba to baza'a karba mashi ba, kuma a ranar lahira yana daga cikin masu asara ).
Al-kur'ani mai tsarki wanda yake a hannun mu, shi kadai ne littafin da Allah ya saukar.
Mu munyi imani da littafin Al-taurah da kuma Al-injila, ammafa Injilar da ke hannun mutane a yau ba'ita Allah ya saukarwa annabi Isa ba, haka kuma Attaurar yau ba'itace wacce Allah ya saukarwa annabi Musa ba.
Dalili kuwa shi ne an ambaci sunan Annabi Muhammad acikin Attaura da kuma Injila ta gaskiyar. A yanzu baka samun sunannashi a cikinsu, kenan ban a gaskiya bane.
Annabi Musa amincin Allah su tabbata a gareshi,ya gayawa jama'ar shi cewa akwai wani annabi da zaizo a bayana sunan shi Muhammad, shima annabi Isa ya gayawa Banu-Isra'ila cewa akwai wani annabi da zaizo a bayana sunanshi Ahmad.
Saboda haka suk wani littafin Attaura ko Injila da babu sunan annabi Muhammad to ba na kwaraibane.
Acikin Al-kur'ani an ambaci Annabi Isa har so "25", bamu iya goge daya daga cikin wadannan sunaye.
Annabi Musa kuwa an ambaceshi har so "138", bamu da ikon share daya daga cikin wadannan sunaye.
Maryam an ambaci sunanta so "39" a cikin Al-kur'ani.
Domin girmamawa da kuma tsarkake wadannan Annabawa, duk musulmin da baiyi imani da annabi Isa ko Musa ba ba'a kiran shi musulmi.
Al-kur'ani shi ne littafin gaskiya wanda ba'a share ko da kalma daya daga cikin shi bs.
Ya zamo wajibi mu nemi Attaura wacce Allah ya saukar ga annabi Musa, da kuma Injila wacce Allah ya saukar ga annabi Isa, sai dai kash inane zamu same su?
Abin takaici litattafan kwarai an batar da su, wadanda ke hannu a halin yanzu mutane suka rubuta su.
An haifi annabi Muhammad (S.A.W.)ne a ranar goma sha uku ga watan Aprilu na shekarun "571" ga haihuwar annabi Isa amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kuma rayu a duniya kimanin shekaru "63" wato kenan ya rasu a shekarun "634" ga haihuwar annabi Isa.
Sabo da menene muke amfani da lissafin haihuwar annabi Isa – kalanda-? Saboda munyi imanin cewa haihuwar shi tafi karfin hankali – Mu'ujiza-
An haifeshi ne ba tare da uba ba, wannan lamari ya fi karfin tunanin dan'adam .. bayan wannan kuma annabi Isa ya fara magana net un yana jariri a cikin tsumman goyo, ya kuma raya mamaci cikin ikon Allah, ya warkar da maras lafiya cikin ikon Allah, ya ya hura rai ga wani butum-butumin tsuntsu da izinin Allah, ya roki Allah ya saukar mashi da kabaki daga sama, nan take Allah ya saukar.
Wannan al'amari akwai shi da abin mamaki, ganin haka ne muke amfani da shi wajan lisafin kwanaki, bayan shudewar shekaru dubu biyu da bakwai.
Amma fa akwi wani abin mamakin da yake hakkin mu ne muyi amfani da shi wajan lissafin kwanaki, wato rasuwar annabi Muhammad, akan wane dalili? Saboda Muhammad shi ne karshan annabawa. Kuam Allah ya yanke turo da sako zuwa bil'adam tun daga rasuwar tashi.
Wannan rana ta goma sha biyu ga watan Rabiyul Auwal na shekarun "570" ko "571" ga haihuwar annabi Isa, ranace mai girma, a cikinta ne aka haifi annabi Muhammad kuma a irin wannan rana ce ya rasu.
Duk mutumin da baya amfani da lissafin haihuwar annabi Isa da kuma rasuwar annabi Muhammad to yana gaba da annabawan Allah.
Kabilanci ne yasa duniya bata amfani da lissafin rasuwar karshan annabawa.
Allah da kuma Mala'ikun shi sun yiwa annabi Muhammad Salati .. Allah yace : "Allah da Mala'ikun shi suna yiwa annbi salati" game kuwa da sauran annabawa kuwa sai Allah yace : "Aminci su tabbata a gare su"
Allah ya umarci annabi Muhammad da yayi tafiyar dare daga masallaci mai haramci na Makka zuwa masallaci mai nisa na Baitil-Makdis .. ya kuma nuna mishi ayoyi masu girma, Allah yace : ( kuma lalle ya gan shi, a wani lokacin saukarsa ) ( A wurin da magaryar tukewa take ) ( A inda taken, nan Aljannar makoma take ) ( Lokacin da abin da yake rufe magaryar tukewa ya rufe ta )
Wadannan suna daga cikin mu'ujizar da Allah ya bawa annabi Muhammad, duk mutumin day a kirkiri wasu mu'jizozi daban ya jinginasu gare shi ya kafirta.
Wadan da suke batanci ga Annabi Muhammad a kasashan yankin sikandinabia-Scandinavia- kabilanci ne kuma jahilai ne, basu san cewa shi ne annabin bil'adama baki dayansu ba.
Abin tambaya anan shin al'ummarScandinaviasunyi imani da annabi Isa? Ko alama .. tunda dai har suka iya zagin annabin Allah.
A tunanin su Muhammad annabin Lrabawa ne, haka ne amma kuma suma annabin su ne.
Allah (S.W.T.) ya yi alkawarin cewa addinin da annabi Muhammad ya zo da shi zai rinjayi sauran addinai koda yanScandinaviabasu so ba.
Allah yace : (Wadanda suke suna bin Manzo, Annabi, wanda bai karatu ko rubutu, wanda suke samun sa rubuce a wurins , a cikin Attaura da Linjila, sai dai kashi Attaura da kuma Linjila a yau ba wannan magana an shafe.
Allah yace : (Kuma a lokacin da Isa dan Maryama ya ce, "Ya Bani Isra'ila! Lalle ni, Manzon Allah ne zuwa gare ku, mai gaskata abin da ke gaba gare ni na Attaura, kuma mai bayar da bushara da wani Manzo da ke zuwa a bayana, sunansa Ahmad ..)
Tun daga lokacin Annabi Ibrahim aka fara zuwa aikin haji a Makka mai tsarki .. Ita kuwa dakin Ka'aba gabanin annabi Ibrahim aka gidata domin bil'adam su ziyarce shi da niyyar hajji ba wai mabiya Annabi Muhammad kadai ba.
Allah ya ce : ( Kuma Allah ya wajabtawa mutane ziyartar dakin shi, ga wanda ya sami ikon zuwa gare shi.. ) Allah bai ce ya wajabta hajji akan Larabawa ba, a'a akan mutane yace.
Allah ya ce : ( Kuma lalle ne, daki na farko da aka aza domin mutane, shi be wanda ke Bakka ..) Makka. Allah bai ce ga Larabawa ba, cewa yayi mutane.
Wa ya isa ya hana mutane ziyartar dakin Allah? Allah y ace : ( Lalle ne wadanda suka kafirta kuma suka kare mutane daga hanyar Allah da masallaci mai al-farma wanda muka sanya shi ga mutane .. )
Allah y ace : ( Yak u wadanda suka yi imani! Abin sani kawai, mushirikai najasa ne, saboda haka kada su kusanci masallaci Mai alfarma ..)
Idan Papa Roma yace yana so ya yi dawafi a dakin Allah Ka'aba, mai zai faru?
Sai a hana shi, idan ya tambaya wane dalili ne zaku hanani? Sai a diba cikin kura'ni a bashi amsa da wannan Aya : ( Mushirikai najasa ne ..) shi kuma sai ya kada baki yace : Ni ba mushiriki ban e kuma ba najasa ban e, saboda haka hakkina ne na yi Dawafi, domin wannan dakin na Allah neb a na Larabawa ban e.
Haka kuma idan shugaban kasar Amurka ya zo shima ya bukaci yayi dawafi a Ka'aba, shin akwai wanda ya isa ya hana shi, ya kuma ce kai mushiriki ne?
Saboda haka abubuwan da ake yi a halin yanzu ya sabawa Al-kur'ani mai tsarki.
Mushiki kawai ake da ikon hana shi dawafi a Ka'aba, sauran muta ne kuwa hakkin su ne suyi dawafi, duk mutumin da ya hana wani mutum daban yin dawafi a Ka'aba to ya kafirta, Allah y ace : ( Lalle ne wadanda suka kafirta kuma suka kare mutane daga bin hanyar Allah da masallaci mai al-farma ..)
Duk mutumin da ke da ikon zuwa Ka'aba da nufin yin dawafi hakkin shi ne, Allah y ace : ( Kuma alokacin da muka sanya dakin ya zamo makoma ga mutane ..)
Bayanin karshe a wannan rana mai girma shi game da batun Sunna da kuma Shi'a.
Shi'a da kuma Sharifai na fuskantar danniya da kuma cin zarafi a kasashan Larabawa .. badan komai ba sai donmin sun ce sayyidina Ali shi ya fi dacewa day a zamo halifan Manzon Allah na farko.
Darikun Shi'a kamar Al-Baharah da Baha'iyya da Nazzariyyah da Duruz da Nusairiyyah da Zaidiyyah da kuma Kadiyaniyyah, dukkannin sun a fuskantar cin zarafi.
A kasashe da dama an hana yan shi'a su shiga takarar shugan kasa, ko kuma a nada su sarakuna.
Haka suma Sharifai, saboda kasancewar su suna da dangantaka da iyalan gidan Annabi (S.A.W.)
Ni a nan ina magana ne game da hakkin siyasa ba ina magana ne game da hukuncin addini ba.
Wannan kasaUgandata bawa darikun shi'a mafaka wadanda aka koro su daga kasarIndia, dariku kamar su : Al-Bahara da Isma'iliyya.
Kowa yaje ya yi imani da Allah kamar yadda ya zaba, amma harka siyasa dukkanninmu daya muke a dokar mulki ta kasa.
Ya zamo dole mu koma ga tsohon tsari irin na tsohuwar daular musulumci ta Fatimiyya saboda mu sami damar kare wadannan dariku daga danniyar da suke fuskanta.
Zamu cigaba da raya wannan rana mai girma, har sai addinin Allah ya yi rinjaye, an fahimci cewa annabi Muhammad manzon Allah ne ya zuwa ga yan'adam baki daya.
Allah ya maimaita mana a min . Wassalamu Alaikum